Wasu yan Bindiga sunkai Farmaki kauyen bari dake karamar hukumar Roga ta jihar kano, inda suka sace wani basarake da kuma wata matar Aure.
Mutanen da aka sace sunhadar da shehu Bello Bari (yariman Bari) sai kuma kanwa ga dagacin garin na bari, kuma matar Aure maisuna Binta Abdulkadir.
Wani mazaunin kauyen, Sulaiman Abdulkadir, ya shaida cewa ko kafin wannan harin, an taba sace dan uwan matar Auren, kafin daga bisani a sake shi.
Yace :"muna cikin matsananciyar damuwa da wannan harin gaskiya, saboda har yanzu babu Wanda ya tuntubi iyalan su.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, kakakin rundunar yan sanda na jihar kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, yace bashida masaniya akan wannan harin.
Comments
Post a Comment