Alkalin wata kotun musulunci dakej ahar Kaduna, Malam Salisu Abubakar Tureta, yace zai biyawa wani Saurayi Sadakin domin ya auri buduruwarsa wadda iyayenta suka Makashi a kotu.
Alkalin kuma ya bukaci matashin da yaje
yayi shawara kan auren buduruwartasa,
sannan ya dawo ya sanar da kotu matsayar
sa ranar 6 ga watan satumba, 2022.
Mahaifiyar budurwar ce ta maka salele a
kotu domin tilasta shi ya auri yar tata.
"Unguwarmu daya dashi, kullum sai yazo
zance alhalin bainemi izininmu ba mu
iyayenta.
"Naje na samu mahaifiyar sa nayi mata
magana, amma tace danta bai Isa aure ba.
"Daganan saiya dena zuwa, yakoma kiranta
a waya yace su hadu a wani wurin.
"Nikuma bana son ya lalata mun 'ya, shiyasa
na kawoshi kotu".
Sai dai Salele yace shifa da gaske yana son
'yar tata, amma sai nan da shekara biyu
zaiyi aure.
"Ni dalibi ne a Jami'a kuma idan nayi aure
hankalina zai rabu biyu.
"Kuma ko kudin sadaki bani dashi, yanzu ma
iyayena ke kuladani". Inji shi.
Comments
Post a Comment