By:- mujahid Muhammad tijjani
Ambaliyar ruwa ta lalata yankuna 225 a kananan hukumomi 31 dake kano da jigawa a cewar hukumar bayar da again gaggawa ( NEMA)
Babban jami'in NEMA mai kula da kano da
jigawa, Dr.Nuradden Abdullahi ya sanar da
hakan yayin zantawa da manema labarai a
ranar Sanar.
A cewarsa ambaliyar nada nasaba ne da
ruwan Sama na mako da ake tafkawa tun
daga watan yuli zuwa yanzu.
Yace wannan yanayi Wanda ba yanzu aka
soma fuskantar Saba, ya tilasrawa mutane
da dana rasa matsuguni da sasu yin hijira
zuwa wasu yankuna na Arewacin kasar.
Kananan hukumomin da ambaliyar ruwan
ta shafa a kano sun hada da Tudun Wada,
Doguwa, Kibiya, Kiru, Gwale, Danbatta,
Bagwai, Ajingi, Albasu, Shanono , Tsanyawa,
Rimin Gado, da Dawakin Kudu.
A jihar jigawa kuma akwai kananan
hukumomi irinsu, Kafin Hausa, Malam
Madori, Hadeja, Guri, Auyo, Birniwa, Jahun,
Miga, Kiyawa, Birnin Kudu, Babura,
Gwaram, Kaugama, Dutse, da Kirikasamma.
Abdullahi ya ce ambaliyar ta lalata gidaje da
gine-gine da gonaki da sauran tarin
dukiyoyi .
A kwanakin baya ne aka yi ruwan Sama
kamar da bakin kwarya da ya lalata
yankuna da dama a jihohin kano da jigawa,
Wanda yayi sanadin asarar rayuka da
dukiyoyi na miliyoyin naira.
Aminiya ta rawaito cewa, ambaliyar ruwan
na zuwa ne a yayin da NEMA ke cigaba da
gargadin masu ruwa da tsaki da su dauki
matakan dasuka dace domin kaucewa
ambaliyar ruwan dake addabar al'umma
daban-daban a halin yanzu.
A farkon wannan watan ne Hukumar
hasashen yanayi (NiMet) ta Sanar da cewa
ana sa ran saukar ruwan Sama kusan duk
Rana a jihohin arewa 19 ciki harda kano da
jigawa a tsakanin Agusta zuwa satumba
shekara ta 2022.
Comments
Post a Comment