Wani mamakon ruwan Sama da aka tafka
yayi sanadin raba daruruwan mutanen
kauyen karnaya dake jihar Jigawa da
muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa.
Aminiya ta wallafa cewa, ambaliyar ta
kuma lalata gidaje fiye da rabin gidajen
dake kauyen.
Kauyen na Karnaya na dab da Dutsen, wato
babban birnin jihar.
Ambaliyar ruwan dai wacce aka farata tun
misalin karfe 6 na yammacin Asabar ta
tayar da mutanen kauyen tsaye har zuwa
yammacin lahadi, inda suka koma neman
mafaka a ajujuwan makarantun yankin.
Da yake zantawa da manema labarai, daya
daga cikin mazauna kauyen, Ado karnaya,
ya ce,
"Tun jiya har yanzu ban samu naci abinci ko
kuma na rintsa ba. Idonmu biyu muna
kokarin tallafawa 'yan uwanmu."
Da wani wakilin Aminiya ya tuntubi
shugaban masu bada agajin gaggawa na
jihar Jigawa ( SEMA), Yusuf Sani Babura, ya
tabbatar da faruwar lamarin.
Yace ambaliyar ta tashi kusan ilahirin garin,
yayin da su kuma suke kokarin Samar da
matsugunai da abinci ga mutanen da
lamarin ya shafa.
"Gaskiya ne ilahirin kauyen ruwa ya tafi da
shi. Yanzu haka ina wajen tare da
ma'aikatana muna kokarin basu tallafin
abinci da muhallai.
Comments
Post a Comment