An Cafke Wani mutum dauke da bundigogi 8 ya shiga hannu a tashar motar zuba dake Abuja.
'yan banga ne dai suka Cafke mutumin a ranar Laraba a lokacin da yake kokarin bada sakon bindigogin domin a kai masa su zuwa jahar kano.
Kwamandan 'yan bangar na yankin zuba, yahaya Madaki, yace dubun mutumin ta cikane bayan yaje tashar ya Nemi a hada shi da direban dake Lodi zai bada sakon makaman akai masa su kano.
"Sai Aka nuna mishi direba dake lodi a lokacin sai ya bawa direban kayan a cikin kwali da lambar wayar Wanda zai karbi kayan a kano.
Akace masa kudin kayansa nera 10,000 Wanda anan take ya biya.
Sai direban ya Nemi tabbatar da kayan dake cikin kwalin amma mutumin ya ki, sai yayi kokarin tserewa amma jama'a suka rutsa shi." Inji Madaki.
Yace da aka buncika sai Aka samu bindigogi 5 kirar AK-47 da wasu kirar pump action a cikin kwalin.
Rahotonni sun bayyana cewa DPO na yankin zuba, CSP Oscar Moses, da Kansa ya jagoranci tarar mutumin.
Sai dai da aka tuntubeshi (DPO) bai samu damar magana ba, amma yace asamu kakakin rundunar 'yan sandan Abuja, DSP Josephine Adeh, wadda ita kuma tace zata bincika tayi magana Karin haske.
Sai dai kuma har aka kammala hada wannan rahoton ba aji daga gareta ba.
Comments
Post a Comment