A safiyar yau ne aka wayi gari da wata magana Akan shehin malamin nan kuma Limamin masallacin kasa wato professor Ibrahim Maqari.
Maganar na nuni ne da cewa kasar Saudiya ta nada shehin malamin Limamin masallacin Harami dake garin.
yace, a safiyar yau ya amshi Kira daga
mutane daban-daban akan lamarin kuma
ya kara da cewa kila masu yi masa fatan
alheri ne suka kirkiri wannan labarin
kokuma suna ne yazo daya.
Amma yace yana godiya ga dukkanin masu
yimasa fatan alkhairin da kyakyawan zato.
Comments
Post a Comment