Biyo bayan ambaliyar ruwan da aka samu a kasuwar Kantin Kwari dake kano, Gwamnan jahar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bada Umarnin fara rusa duk wani gini da akayi akan hanyar ruwa a cikin kasuwar.
Umarnin kuma zai shafi kwatar kwarin Gogau dake cikin birnin na kano.
Sauran guraren da za'a rusa sune ilahirin gine gine da akayi akan kwalbatoci dake kewaye da kasuwar don a bawa ruwan Sama da shara damar damar wucewa batare da wata matsalaba.
Kwamishinan yada labarai na jahar, Malam Muhammad Garba, ne yasanar da hakan,lokacin da yake yiwa 'yan jaridar fadar gomnatin jihar kano jawabi kan batutuwan da majalissar zartarwar jahar ta tattauna ranar laraba.
Bayan karbar rahotonni akan irin barnar da ambaliyar ta haifar a kuwar ta Kwari, wanda kwamishinan Ayyuka, Eng. Idris Wada Saleh dana muhalli, Kabiru Ibrahim Getso, suka gabatar. Majalissar takuma ba da Umarnin cire dukkan tebur da kuma rumfunan wucin gadi da aka kafa akan magudanan ruwa na cikin kasuwar ba tare da bata lokaci ba.
Idan za a iya tunawa, kasuwar ta fuskanci mummunar ambaliyar ruwa a makon nan, wacce tayi sanadin tafka asara ta manyan miliyoyin Nairori.
Comments
Post a Comment