Rundunar'yan sandan jahar Kano ta Kama wata matashiya mai shekaru 27, bisa zargin sheka wa wani Matashi Lawan Inuwa Ibrahim, dan shekaru 25 tafasasshen ruwan shayi a jikinsa.
Jami'in Hulda da jama'a na rundunar 'Yan Sanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar yayin ganawa da manema labarai a juma'ar nan.
Ya bayyana cewa rundunar ta sami korafi ne daga wasu mutane a unguwar Rimin Auzinawa dake karamar hukumar Ungogo a ranar 11 ga watan satumba.
Ya kara da cewa "Bayan samun korafin ne rundunar ta tura jami'an ta karkashin baturen 'Yan Sanda na unguwar rijiyar zaki, CSP Usman Abdullahi, inda suka garzaya da matashin asibiti tare da Cafke wacce ake zargin."
"Bayan kaishi asibitin kwararru na Murtala Muhammad ne aka kwantar dashi kuma likitoci suka shiga yimasa magabi a fuska da hannunsa da cikinsa dama guraren da kunar ta shafa.
Karin labarai
How to apply for N-Power B Tech
'Yan bindiga sun Kama wani barawo kuma sun dankashi ga hukuma
A nata bangaren, wacce ake zargin at amsa cewa, ta watsa masa ruwan kuma tayi hakanne sakamakon rikici daya barke a tskaninsu.
A cewar ta tana zargin Matashin da kashe mata aure ta hanyar Kai gulmace-gulmace wajen mijinta.
Matar tace matashin ne ya soma yunkurin sheka mata ruwan zafin a lokacin da kokawa ta barke a tskaninsu.
Comments
Post a Comment