Gwamnatin tarayyar Nigeria tayi Karin haske akan yadda ake musgunawa 'yan Nigeria din a kasar hadaddiyar daular larabawa wato Dubai (UAE).
A makonnin baya-bayan nan ne aka samu a kafafen sada zumunta sunyi ta yada rahotonni cin zarafin da ake yiwa 'yan Nigeria a kasar.
Da take tsokaci kan batun, shugabar hukumar 'yan Nigeria mazauna kasashen waje (NIDCOM), Mrs Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana cewa, a kwanakin baya Hukumomin kasar ta Dubai UAE sun fitar da sababbin ka'idoji na neman biza ga mutanen kasa da shekara 40.
Tace, da yawa daga cikin 'yan Nigeria a yanzu suna kokarin kaucewa ka'idojin ta hanyar neman neman takardar izinin Zama da iyalan su "biza ta Iyali" maimakon ba da haske kan irin bizar da suke nema.
Ta bayyana cewa, dole ne a Samar da bayanan banki na gaskiya na tsawon shida, da bayanan masauki da tikitin dawowa, idan an iso kasar.
Aminiya ta rawaito cewa, Hukumomin UAE sun tsaurara dokokin ba da takardar Zama ta biza ga 'yan Nigeria biyu bayan tarzomar da wasu 'yan Nigeria suka tasar a kasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Dabiri-Erewa ta ce "ku tuna gargadin da aka fitar a baya-bayan nan". A yanzu dai gwamnatin hadaddiyar daular larabawa wato Dubai UAE ta bullo da wani sabon tsarin biza kuma ta daina bayar da bizar yawon bude Ido ga wadanda suke kasa da shekara 40, sai dai wadanda ke neman bizar Iyali.
Comments
Post a Comment