Tirka tirka kenan
A wani yanayi mai cike da daure Kai, 'yan
bindiga a jihar Katsina Sun Kama wani
dan Jari bola yana sace sace a kauyen da
mutanen garin suka suka bari.
Kafar yada labarai ta PRNigeria ta rawaito
cewa wanda ake zargin, wanda matashine
ya kware wajen cire rodika da karafa daga
ginin mutane a wani kauyen.
Kafar dai ta rawaito cewa 'yan bindigar sun
Kama matashin ne a lokacin da suka futo
sintiri akan baburansu.
A wani bidiyo da kafar ta samu, an ga 'yan
bindigar suna gabatar dashi tare da
karafan daya sata a gaban wani shugaban
al'umma na kauyen.
Sai dai kafar bata iya tantance locakin da
aka nadi bidiyon ba.
"Baka San sata laifi ba ce? Kayi sa,a zamu
mikaka gaban Hukuma, da kashe ka
zamuyi" inji 'yan bindigar.
'Yan ta'addan dai, wadanda aka gani a
bidiyon, rike da muggan makamai, sun
gargadi shugaban daya tabbatar an
hukunta barawon daidai da doka don ya
Zama izina ga masu Hali irin nasa.
Kazalika, majiyar tace ba wai kawai damka
matashin suka yi ga Hukuma ba, sun kuma
tabbatar da cewa daga bisani jami'an tsaro
sunyi awon gaba da shi don a titsiye shi.
Comments
Post a Comment