Kwararru sun bayyana cewa, wani nau'in sauro wanda baya Jin maganin kashe Kwari, kuma wanda ya dade da wanzuwa a kudancin Asia ya yadu zuwa wasu kasashen Africa, ciki harda Djibout, Ethiopia, Sudan, dakuma Nigeria.
Masana sunyi gargadin cewa sauron Zai iya haddasa karuwar masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya, cutar data dade tana sanadin asarar rayukan jama'a musamman ma kananun yara a nahiyar Afirka.
Dacka Abdullahi Isa Kauran-mata, shine shugaban cibiyar dake yaki da cututtuka masu yaduwa ta jihar kano, ya shidawa BBC cewa shi wannan nau'in sauron sabo ne wanda ke a yankin Asia dakuma kasashen Larabawa.
Yace sakamakon mu'amula ta yau da gobe tsakanin mutanen yankin Asia dana Afirka, yasa shi wannan sauro ya shigo yankin Afirka, kuma tun daga lokacin da aka gane ya shigo yankin ke samun karuwar zazzabin cizon sauro.
Likitan yace "tuni wannan nau'in sauron ya bulla Somalia, Sudan dakuma Nigeria, inda a shekara ta 2020 aka gano irinsa.
Dakta Abdullahi Isa Kauran-mata, yace shi irin wannan sauron Zai iya rayuwa har cikin birane ba kamar sauran sauraye da suka fi rayuwa a kauyuka ba.
Likitan yace, a yanzu babu maganin wannan sauron sadidan, amma ana gudanar da buncike akan irin maganin da Zai rinka yiwa mutane maganin cutar zazzabin sauro idan har sun kamu da cutar sakamakon cizon wannan nau'in sauron, saboda shi ba kamar sauran sauraye bane da aka saba dasu wanda kuma magungunan da ake Sha ke maganin cutar idan har sun sanya wa mutane.
Dakta Kauran-mata, yace "dayake yan zun ba a ba'a Kai ga gano maganin wannan sauro ba, to idan ya ciji mutum har ya sanya masa cutar maleriya, to zazzabin Zai iya zafi sosai fiye da irin wanda akeyi idan saurayen da aka basa dasu suka ciji mutum."
Yace kada mutane su tsorata domin tun bayan bayyanar wannan nau'in sauron a Nigeria a 2020, masana suka fara neman maganin sa.
Likitan yace, babban matsalan ita ce idan har wannan sauron ya yada cuta to akan dan Sha wuya Kafin a gano cewa mutum ya kamu da cutar zazzabin cizon sauro.
Duk da cewa ana iya kare Kai da samun waraka, har yanzu cutar maleriya na cigaba da kisa a duniya.
A 'yan shekarun baya-bayan nan ana samun sauyi kan yadda ake yaki da maleriya.
Yara 'yan kasa da shekaru biyar sune rukunin farko da cutar tafi yiwa illa.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta bada shawarwarin kariya daga kamuwa da cutar da dabarun da take ganin sune mafita.
Hanyoyin kariyar sun kasu kaso biyu, akwai amfani da gidan sauro da kuma feshin maganin sauro wanda akasari akafi yi a lokutan dakuma.
Bacci da gidan sauro na rage damar da sauro ke da ita wajen cizon mutum.
Feshin maganin Kwari a gidaje da gine-gine a kalla so daya ko biyu a shekara, na taimako sosai.
Comments
Post a Comment