Wata Tifa makare da Yashi Ta muttsuke akalla mata 6 har lahira a unguwar kaswan fara dake shagari low-cost a garin Maiduguri a ranar
Wani ganau, kola fatai yace tifar tabi takan wata akori kura dake dauka da mutane , nan take ta kashe mata shida wasu da dama kuma suka sami rauni.
Ya bayyana cewa mutanen sun gamu da ajalinsu ne bayan burkin motar ya tsinke a dai dai lokacin da take dauke da Yashi akan hanyar gubio dake gaban waje Maiduguri da misalin karfe goma na safe.
Wani mazaunin unguwar mai suna, IMAN buba ya shaida mana cewa fusatattun matasa sun banka wasu tifofi biyu wuta Sakamakon hatsarin da akayi
A cewarsa, yawan matan da suka rasu a hatsarin sun ka goma , wanda yasasu zanga zangar tare hanyar Maiduguri zuwa Gubio.
Wani shaida yace tifar da kashe matan tana kokarin Shan gaban wata Tifa ne, amma ta kwace ta hau kan akori kurar da matan suke ciki.
Tuni aka Mika jam'i,an tsaro zuwa gurin donin tabbatar da tarzoma
Wakilin daily Trust yayi kokarin Jin ta bakin kakakin rundunar 'Yan Sandan jihar barno , ASP SK, Shatambaya , amma yace masa basu samu rahoto ba
Comments
Post a Comment