Har yanzu Matsalar tsaro na ciga da tabarbarewa a garuruwa da dama na yankunan kananun hukumomin Gumi da Bukkuyum na jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Nigeria.
Yanzu haka fiye da garuruwa 50 na neman Zama kufai a yankunan kananun hukumomin Sakamakon yadda hare-haren'yan bindiga suka tilastawa Al'ummar garuruwan yin gudun hijira zuwa wasu sassan jahar dama makwabtan jahar.
Hakan kuma na afkuwa ne duk da kudaden haraji fiye da naira miliyan dari da 'yan bindigar suka karba a hannun mutanen garuruwan bisa yarjejeniyar 'yan bindigar zasu bari a gudanar da aiyikan noma, a kuma girbe kayan amfanin gona.
Mannir Sani Fura Girke, dan jaridar ne mai bunciken kwakwaf kan harkokin da suka shafa tsaro, ya shaidawa BBC cewa, anyi yarjejeniya da 'yan bindigar dakuma garuruwan 55, inda suka yarda cewa bazasu kara Kai hare-hare ba muddin aka biyasu kudin haraji.
Yace "dukkan garuruwan 55 sai da suka biya kudin su, wasu miliyan uku wasu hudu haka aka tara aka basu naira miliyan 172 da dubu dari biyar.
Dan jaridar yace anaga kamar abin yayi sauki za'a samu damar aikin gona, sai yanzu suka sake dawowa suna Kai hare hare.
Tuni dai jami'an 'yan sandan jahar tace jami'ansu dama sauran jami'an tsaro na sane da irin Matsalar tsaron da ake fuskanta a kananun hukumomin dake Gumi da Bukkuyum.
SP, Muhammad Shehu, shine mai magana da yawun rundunar 'Yan Sanda da ke Zamfara, ya shaidawa BBC cewa, hadin gwiwar jami'an tsaro na nan na daukar matakan da suka dace a wayennan yankunan domin magance matsalar.
Comments
Post a Comment