Hadarin ya afkune a lokacin wani buki a Calabar babban birnin jihar Cross River dake Kudu maso kudancin Nigeria, lamarin da ya janyo mutuwar mutum 13 tare da raunata mutum 24.
Mai magana da yawun rundunar 'Yan Sandan jihar, SP Irene Ugbo, ya sanar da BBC cewar suna cigaba da yunkurin ceto rayukan wadanda abun ya rutsa dasu.
Hadarin dai ya afku ne a ranar Talata a lokacin bikin wasa da Babura da aka gabatar a titin Mery slessor a bogobiri, daya daga cikin manyan hanyoyin da aka tanada domin wasan na bana.
Wani ganau ba jiyau ba yace babur din ya kwacewa matukin dake gudun wuce sa'a, wanda hakan ya sa ya kutsa cikin 'yan kallo.
SP Ugbo, ya ce "wadanda ake zargi na hannunsu bayan faruwar lamarin".
Gwamnan jihar Cross River Farfesa Ben Ayade, ya soke bukin, inda ya bukaci a gaggauta yin binkice kan faruwar al'amarin.
A wata sanarwa da daraktar yada labarai ta jihar, Cristiana Ita, ta ce "gwamnan jihar nason sanin yadda matukin babur din ya samu damar kutsawa inda ake bukin, dukda an rufe hanyar ga mutanen gari.
SP Ugbo, ya ce 'yan sanda sun maido da zaman lafiya bayan faruwar lamarin.
A wasu hotunan bidiyo masu tayar da hankali da ke yawo a kafafen sada zumunta, sun nuna munanan raunukan da wayanda hadarin ya ritsa dasu suka samu.
Bukin hawa babura na daya daga cikin manyan wasanni kalakuwa da akeyi a birnin na Calabar, a jihar wanda tayi fuce wurin wajen shirya irin wayennan bukukuwan.
Gwamnatin jihar ta Cross River ce dai ta dauki nauyin bukin, da ake gudanar wa shekara-shekara, wanda hakan yasa yazama daya daga cikin bukukuwan da yake janyo hankala a Nigeria a karshen ko wacce shekara.
An fara gudanar da bikin dai a shekarar 2004 a matsayin wasan janyo hankulan masu yawon bude ido a birnin Calabar.
A yayin bukin mutuka babura kan gudanar da nau'ukan wasanni da babur iri-iri, domin kayatar da masu kallo.
A duk lokacin da ake gudanar da bikin, akan takaita zurga zurgan ababen hawa a hanyoyin da aka shirya cewa masu wasa da baburan zasu bi.
Comments
Post a Comment