Ga masu wayoyin hannun da suka Jima suna son Susan yadda zasu dora abubuwan su akan Google dan gudun rasasu musamman yayin canja waya ko faduwa ko kuma sace wa to ga yadda zaku Adana abubuwan ku kamar su video, hoto, Waka , daidai sauran su akan Google.
Domin sanin yadda zaku adana video ko hoto ko Waka akan Google drive ku karanta wannan.
Farkon abunda zaku bukata yayin adana kayan ku akan Google shine Google account wato Gmail inkuma mutum bashi da Google account to sai yayi kokari ya bude.
Yadda zaku dora
idan kuka shiga cikin application na kan wayoyin hannun ku zakuga wannan app din mai suna Drive sai ku shigeshi.
Kuna shiga Zai samuku kuyi updating din sai ku danna kuyi updating bayan na Zai shigar daku cikin sa zakuga wani waje da alamar plus agun sai ku danna shi.
Kuna danna wa Zakuga wani abu ya fito a kasa, abun yana kunshe da abubuwa akwai upload acikin sai ku danna upload din.
Kuna danna wa Zai nuno muku inda zaku zabi abin da kuke son dora wa kamar video, audio, hoto, da dai sauran su.
Daga na zaku zabi abun kuke son ajiye wa, walau hoto ko video ko wani abun daban, kuna zaba Zai kaiku cikin abubuwan, in gallery mutum ya zaba Zai kaishi cikin hotuna haka in video ne Zai kaishi cikin videos kawai mutum saiya danna abunda yake son ajiye wa nan take abun Zai dora kansa a kan Google kuma yananan akai koda ace mutum ya rasa wayarsa ne ko ya mata fomatin abunda ya dora yana Kai kuma Zai sauke shi akan wayarsa duk lokacin daya ga dama.
Comments
Post a Comment