'Yan daban kuma sunyi awon gaba da shugaban matasa kan kin biyan su wasu kudade.
Gungun wasu 'yan daba sun tarwatsa taron jam'iyar APC tare da yin awon gaba da tsohon shugaban matasan jam'iyar PDP, kwamared Obaro Matthew Jagogo.
'Yan daban sun tayar da hankalin jama'a ne a gurin taron da kwamared Jagogo ya shirya da nufin sauya sheka zuwa APC a yankin Aladja na jihar Delta.
Sun zargi tsohon shugaban matasan jam'iyar PDP dakin biyansu N400,000 da suke binsa, amma suka shaidawa mahalarta taron cewa basu da matsala dasu.
Daga bisani suka yi waje da dan siyasar, suka casa makadin taron kuma suka lalata rumfunan da aka kayata wajen taron dasu.
Kwamared Jagogo ya shirya taron ne da nufin bayyana fitarsa daga jam'iyar PDP zuwa jam'iyar APC.
Manyan mutane kamar dan takarar majalissar tarayya Collins Egbetamah, Keston Okoro da Cid Williki na daga cikin wayanda ake sa ran zuwansu wajen taron Kafin 'yan daban su tayar da yamutsin.
Shugaban jam'iyar APC na mazaba ta 10 a yankin Aladja, mista Abeyi Lucky, wanda ya halarci taron dob nuna goyon baya ga shugaban matasan yace, basu yi tsammanin za a samu matsala a wajen ba.
"Ba muyi tsammanin faruwar abu mai Kama da haka ba"
Ana fargabar za'a iya samun hatsaniya tsakanin magoya bayan APC da 'yan jam'iyar adawa a yankin.
Sai dai wasu manyan yankin sunyi Kira ga jami'an tsaron yankin, shugaban karamar hukumar Udu, da sauran masu fada aji dasu sanya baki kan lamarin don tabbatar da doka da oda a yankin
Comments
Post a Comment