Kwankwaso ya sami tagomashi mai ban mamaki a yayin da tsofaffin ciyamomin PDP da kansila suka shigo NNPP
. Jam'iyar New Nigeria Peoples Party NNPP, ta sami karuwa na tsaffin ciyamomi da kansila a jahar Gombe
. Daga cikin wayanda suka fuce daga Jam'iyar PDP suka koma NNPP a baya-bayan nan akwai tsaffin ciyamomi na kananan hukumomin, Billiri, Kwami da Nafada
. Sauran sun hadar da tsohon kansila daga mazabar Tal da ke daga mazabar karamar hukumar Billiri daga shekarar 2013 zuwa 2015.
Ayayin da babban zaben shekarar 2023 ke dada karatowa Jam'iyar New Nigeria Peoples Party NNPP, naci gaba da samin sabbin mambobi daga Jam'iyun APC da PDP.
A wannan lamarin na baya bayan nan ma tsofaffin shuwagabannin kananan hukumomi hudu ne daga Billiri, Kwami da Nafada da kuma tsoha kansila ne suka fita daga PDP suka koma NNPP.
Sun shiga NNPP ne bayan taron da dan takarar gwamna na NNPP a babban zaben shekarar 2023 dake tafe.
An tattaro cewa sabbin mambobin na NNPP za suyi aiki tukuru domin ganin cewa yan takarar ta jam'iyar NNPP da dan takarar ta na shugaban kasa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso sunyi nasara a zaben 2023.
Karanta Shugabancin Kasa Na 2023: Kwankwaso ya bayyana matsayar sa ta karshe kan janyewar takara
Good luck
Comments
Post a Comment