"Kawai farkawa nayi na ganni da fasasshen ido a asibiti."
Ana zargin Yan bijilan da fasa Idon wata amarya mai suna Khadija Abdullahi, lokacin da ake tsaka da bikinta a Garin dantamashe dake karamar hukumar Ungogo ta jihar kano
Lamarin dai ya farune a karshen makon da ya gabata, inda aka fasa mata ido daya, a daidai lokacin da ya kamata ace ana shirin kaita dakin mijinta.
Acewar shedun gani da ido, an gayyato Yan bijilan dinne domin su huna taron Fatin da akeyi, wanda amarya ta shirya.
Saidai Lamarin ya rikida ne ya koma tarzoma, inda aka dinga jifa da duwatsu, har daya daga cikin su ya samu amarya a ido.
Wasu majiyoyin sun shaidawa manema labarai cewa Yan unguwa ne suka gayyato Yan bijilan din, bayan hana duk wani fati da dattawan garin sukayi.
Amarya Khadija ta shaidawa manema labarai batasan lokacin da mutanen suka zoba kawai dai ta farka me ta ganta a gadon asibiti.
Tace Muna tsaka da bikin mu ne na hango Yan bijilan din kimanin su goma, suna korar mutane suna cewa baza ayi a.
"daga Nan ban San meya faru ba, kawai na farka ne na ganni kwance a gadon asibiti ne da fasasshen ido." inji ta
Shima dai angon Khadija, Hamisu Bala, ya bayyana lamarin a matsayin wani yunkuri na tarwatsa musu farin cikin su da gangan, inda yayi kira da hukumomi dasu kwatowa amaryar tasa yancin ta.
To Saidai Yan bijilan din sun nesanta kansu da zargin aika-aika, inda sukace sabanin tsakanin yan unguwar ne da kwamatin da ya hana shagalin bikin.
A cewar kwamandan kungiyar na karamar hukumar, Naziru Abubakar Adamu, "Babu abinda mukayi a wajen, yanzu haka maganar da mukeyi da Kai muna ofishin Yan Sanda tare da duk mutanen da lamarin ya shafa"
To sai dai rundunar Yan sandan jihar kano sunce tuni suka cafke mutum biyu akan Lamarin, kuma za'a tisa keyarsu zuwa kotu da zarar sun kammala binkice
Comments
Post a Comment