. Sawma da watanni shida kenan Yan Nigeria suna fama da tsadar man Fetur wanda taki ci taki cinyewa.
. Bayan watanni gwamnati ta kara farashin man Fetur inda gidajen man kamfanin NNPCL suka koma saida shi duk Lita N190
. A mafi akasarin gidajen man arewa an dade ana saida litar man fetur har Sama da N300
Jiragen ruwa sun dira a legas dauke da litan man fetur miliyan 98.8 a karshen makon nan, bayanai daga hukumar jiragen ruwa NPA nuna.
Bayanai sun nuna cewa jirgin ruwan da aka yiwa lakabi da Antares 1 ya dira a tashar ruwan legas ranar juma'a da tan 36,000 na man fetur.
Jirgin ocean Nirvana ya dira da ton 36, 932 na man fetur ranar juma'ar dai, sannan kuma jirgin Zonda ya dira da ton 25,882 na man fetur ranan Alhamis.
Haka zalika ana sauraro ton 4,758 na man fetur ya isa legas ranar litinin 23 ga watan junairu, 2023.
Bugu da kari ana kyautata zaton jirgin M/T Montago ya Isa da ton 25,000 na man Gas (Ago) da ton 5000 na man jirgin Sama (Jet A1) ranar juma'ar.
Yayinda jirgin M/T Berners ya dira da ton 14,500 na JET A1 da AGO ranar Asabar.
Ko a jiya Lahadi, bayanan hukumar NPA sun nuna cewa jiragen ruwa biyu; M/T Alfred Temile da M/T sapet zasu dira dauke da iskar gas ton 12,000.
Bayan wata da watanni Yan Nigeria na fama da wahala da tsadar man Fetur, gwamnatin tarayya ta amince da Karin naira 15 akan litar man fetur.
Farashin litar mai ya tashi yanzu daga N180 zuwa N195.
Kawo ranar Juma'a 20, ga watan Junairu 2023, tace mafi yawan gidajen mai suna siyar da fetur ne a farashin daya zarce haka rahoton vanguard.
Da alamu gidajen man dake karkashin kungiyar Yan kasuwa na MOMAN sunbi wannan umarni, kuma sun canja farashin litarsu kamar yadda akayi umarni.
Comments
Post a Comment