Hukumomi sun sha zargin Tukur Mamu da goyon bayan ta'addanci.
Wata babbar kotu a jahar Kaduna, ta bayar da umarnin gurfanar da mawallafin jaridar Desert Herald, Alhaji Tukur Mamu a gaban Kuliya.
Kotu ta nemi hukumar tsaro ta farin Kaya reshen jahar Kaduna (SSS) da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami dasu gaggauta gurfanar da Mamun ne tare da wasu mutum biyar.
Bayanai sun nuna cewa ababen zargin da kotu ta nemi a gurfanar dasu bisa ga madogara ta binkice da akayi a kansu sun hada da; Tukur Mamu, Faisal Tukur Mamu, Ibrahim Hussain Tinja, Abdullahi Mashi, Mubarak Hussain Tinja da kuma Yahaya Bello.
Da yake zartar da hukunci kan karar mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Disamba, 2022, Alkalin kotun shari'ar E. Andow, yace kundin tsarin mulkin Nigeria yayi tanadin baiwa duk wani wanda ake zargi 'yancin gurfanar dashi a gaban Kuliya hadi da tuhume-tuhume da masu Kara zasu gabata.
Umarnin kotun na zuwa ne watanni bayan da jami' an tsaro na kasa da kasa na interpol suka cafke tsohon mai shiga tsakanin gwamnati da Yan ta'adda a kokarin kubutar da fasinjojin jirgin kasan nan na Abuja zuwa Kaduna da aka sace a watan Maris a bara.
A watan Satumbar bara ne aka kama Mamu a birnin Alkahira na kasar Masar yayin da yake jiran jirgi domin tafiya kasar Saudiya inda zai gudanar da aikin umara.
Comments
Post a Comment