Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar New Nigeria Peoples Party NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana wayanda ke baza jita jitar majarsa da wata jam'iyar a matsayin Yan siyasa marasa madafa.
Kwankwaso ya bayyana hakane ranar 8 ga watan disamba yayin da yake magana da manema labarai a Abeokuta bayan ya gama jawabi ga mambobin NNPP a sakateriyar jam'iyar dake babban birnin jihar.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar NNPP ya karyata cewa yana shirin yin maja da wata jam'iyar ko wani dan takarar gabanin babban zaben 2023
Comments
Post a Comment