Murja zatayi sharar Asibiti, abokanta kuma zasu rika share masallaci.
Kotun shari'ar musulunci dake Zaman ta a filin Hokey ta yankewa jarumar nan ta Tiktok wato Murja Ibrahim Kunya da abokanta hukuncin sharar masallaci da kuma asibiti.
Abokan Murja maza, wadanda aka gurfanar dasu tare da ita, Ashiru Idris Mai wushirya, Aminu BBC da kuma Sadik Shehu Shariff zasu dunga sharar masallacin Murtala da ke Kano, da bandakunan sa na tsahon mako uku.
Ita kuma Murja zata dunga share asibitin Murtala, ta rika zuwa tana yin awa 8 kullum. a ofishin hisba, kuma ta goge wasu bidiyoyin ta a shafukan sada zumunta, sannan an haramta mata gudanar da taron jama'a.
Kotu ta yanke musu hukuncin ne a shari'ar da aka gurfanar dasu kan zargin Yada batsa a kafar Tiktok da kuma bata tarbiya, zargin da suka musanta.
Gabanin zaman Kotun na ranar Alhamis, saida Alkali, Mai shari'a Abdullahi Halliru, ya turasu zaman wakafi zuwa gidan yari akan zargin.
A zaman na ranar Alhamis, mai gabatar da kara, lauyan gwamnatin jahar Kano, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya roki Kotun da'a sake karantawa Murja takardar tuhumar da ake mata nayin batsa, ta yar da hankali da barazanar Zaman lafiya a cikin Al'umma, wanda hakan ya sabawa sashi na 355 da kuma na 33 dana 275 na kundin shari'ar musulunci.
Sannan ya gabatarwa da Kotun takardar yarjejeniya ta sulhu wacce Murja ta rubuta kan cewa ta amsa laifin ta, ta hannun lauyan ta Barista A E Saka.
Daga nan ne mai shari'a, Abdullahi Halliru yayi umarnin da a karanta mata takardar hukuncinsa.
Takardar ta kunshi cewa dole ne ita wacce ake tuhuma ta goge dukkan wani bidiyo ko sauti data wallafa mai dauke da batsa data wallafa a shafinta na sada zumunta.
An kuma haramta wa Murja shirya duk wani nau'in taro na jama'a da zai Iya jawo batanci ko bata tarbiya ko tayar da tarzoma ko kuma tada hankulan jama'a.
Sai kuma sharadin zuwa ofishin hukumar hisba a duk ranar Alhamis da Litinin daga karfe 12 na rana zuwa 5 na yamma har na tsahon wata shida.
Haka kuma zata ringa gabatar da kanta a kotu duk bayan wata daya tare da ma'aikacin hukumar hisba.
Takardar Kotun tace sabawa wadannan sharadun zai iya janyowa a kara mata lokaci akan wanda Kotun ta Sanya mata na wata shida.
Bayan karanta mata ne mai shari'a ya tambaye ta ko ta gamsu, nan take ta amsa da cewa ta gamsu.
Idan za'a Iya tunawa, majissar malamai ce ta jahar Kano takai karar Murja Ibrahim Kunya ga yan'sanda inda su kuma suka gurfanar da ita a gaban kotu.
Ana tuhumar Murja da laifin hada kai da Sunusi Oscar 442 da Safara'u da Dan Maraya da Amude Booth da Samha M Inuwa da Ummi Shakira, wanda yanzu haka suka cika wandon su da iska, inda suke bin wata Waka ta Ado Gwanja da Kawo Dan Sarki inda suke Yada shi a shafukan sada zumunta wanda hakan zai iya bata tarbiyan Al'ummar jihar Kano.
Comments
Post a Comment