Tarihi 5 da Ronaldo ya kafa A wasan Portugal da Liechtenstein.
Ina masoyan dan wasa Cristiano Ronaldo ku karanta dan sani ga garumar rawar da gwanin naku ya taka...
Ronaldo ya jefa kwallo ta 60 a bugun tazara a tarihi.
Cristiano Ronaldo ya bugawa kasarsa ta Portugal wasa na 197, ya kuma ci kwallo biyu a wasan neman shiga Euro 2024, bayan doke Liechtenstein da ci 4 da nema.
Dan wasan mai shekaru 38, shine kan gaba a yawan jefa kwallaye a tawagar a harihi kusan shekara 120 kawo yanzu.
Dan wasan ya fara bugawa kasarsa kwallo ne tun a shekarar 2003, wanda a gasar kofin duniya na 2022 wanda aka buga a Qatar, ya zama na farko da ya zura kwallo a ko wacce gasa a kofin duniya.
Minti takwas da fara wasa Portugal taci kwallo ta hannun Joao cancelo, Minti biyu da komawa zagaye na biyu dan wasa Bernardo silver ya kara ta biyu.
Sai Cristiano Ronaldo ya ci ta ukku a bugun fenariti, sannan ya kara ta huddu a wasan.
Kwallo ta hudu da Ronaldo ya jefa a wasan, a bugun tazara, ita ce cikon ta 60 da irin wannan Salo a tarihi.
Haka kuma tun daga shekarar 2004 kawo yanzu, babu shekarar da tauraron bai jefa ma kasarsa kwallo akalla daya ba.
Ronaldo bai tsaya nan ba, a wasan dai yaci ya ciwa Portugal kwallo cikon ta 100 a duk gasanni wanda ba na sada zumunta ba ne.
A gasar kofin duniya a Qatar da Ronaldo ya buga, shi ne yayi kan-kan-kan da Bader Al-Mutawa, wanda ya yi wa Kuwait fafatawa 196.
Ronaldo ya yi kafada da Dan kwallon Kuwait a yawan bugawa tawagar tamola, a wasan da Morocco ta fitar da Portugal a zagayen quarter final.
Mai balloon d'or biyar ya yi Zaman benci a Qatar a Portugal, sai dai sabon koci, Roberto Martinez ya gayyaci tsohon dan wasan Real Madrid da Juventus.
Ronaldo ya koma taka Leda a gasar kwallon kafa ta Saudia a kungiyar Al Nassr a watan Junairu, bayan da ya raba gari da kungiyar Manchester United ta kasar England.
Comments
Post a Comment