Wanna man yana karawa gashi lafiya, cika da kuma tsayi.
Mata da yawa na fama da zubewar gashi ko karyewarsa, saboda dalilai daban-daban, kuma asarar gashi abune dake ciwa mata da yawa tuwo a kwarya, musamman suna son suga gashinsu da tsayi.
Shiyasa muka kawo muku wannan hadin da zai taimaka muku wajen rage zubewar gashin.
Wannan man yana karawa gashi lafiya, cika da kuma tsayi.
Kayan hadi:
-Kanamfari
-Man kwakwa
-Tafarnuwa
-Albasa
Yadda ake hadin:
A bare Tafarnuwa da Albasa, a daka su tare, a zuba Kanamfari a daddaka su duka.
A samu kwalba mai fadin baki a zuba kayayyakin da aka daka, sai a zuba man kwakwa isasshe a ciki.
Bayan an zuba dakakkiyar Tafarnuwa da Albasa da Kanamfari da kuma man kwakwa a cikin kwalbar, sai a jijjiga sosai sai a ajiye tsawon kwana ukku (3).
Bayan kwana ukkun (3), sai a kara jijjigawa sosai, sai a tatse man a zubashi a wani mazubin daban da ake so.
Shikenan sai a dunga shafawa a gashin da kuma fatar gashin akai - akai.
Wannan man na gyra gashi sosai.
Good luck
Comments
Post a Comment