Binkice ya nuna cewa yaren Hausa shine yare na 11 a jerin yarukan da akafi anfani da su a duniya, kuma na farko a Africa ta yamma.
Yaren Hausa dai yanada masu anfani dashi sama da mutum muliyan 150 da suka warwatsu a kasashe sama da 30 kuma shi yake biyewa faransanci a yawan masu anfani dashi a duniya.
Ana amfani da yaren a kasashe 32 daga cikin kasashen Africa 54 bayan sunyi hijira zuwa can saboda dalilai daban-daban.
Harta a kasar Sudan, binkice ya nuna akwai hausawa kimanin muliyan 10 yan asalin kasar.
Andai fara gudanar da bukin Ranar Hausa ta duniya a shekara ta 2015 a kafafen sada zumunta na zamani.
A lokacin dai, wani ma'aikachin sashen Hausa na BBC, Abubakar Jari da wasu abokansa na suka fara bikin ranar domin samarwa da masu amfani da yaren damar tattauna abubuwan dake ciwa yaren tuwo a kwarya.
Daga bisani a shekarar 2018, an fara gudanar da bukukuwan na zahiri a Gidan Dan Hausa dake jahar Kano dama wasu sassan duniya, ciki harda kasar Ghana.
Wayanda suka kirkiri bikin sunce sunyi hakanne da nufin tunawa Al'ummar hausawa muhimmancin yarensu da kuma tarasu a waje daya domin tattauna yadda za'a inganta shi.
Ya zuwa shekarar 2020, an gudanar da bikin ranar Hausa ta duniya a kasashe sama da 25 na fadin duniya, ciki harda faransa da Saudiya.
Masana dai sunce Hausa na daya daga cikin yarukan da sukafi saurin yaduwa a duniya, inda hatta manyan kanfanonin sadarwa irinsu Facebook, Google dama IOS sai da suka saka shi a jerin yarukan da suke amfani da su.
Ko a 'yan shekarunnan ma, hukumar lafiya ta duniya ta saka yaren Hausa a jerin yarukan da take amfani da su wajen yaki da annobar COVID-19.
Haka zalika, a shekarar 2020 ma, kasar Saudiya ta saka yaren Hausa a jerin yaruka 10 da take amfani da su wajen fassara hudubar Arfa, wanda shine taron addini mafi girma a duniya.
Menene ra'ayinku game da wannan ranar Hausan ta duniya?
Comments
Post a Comment