By:- mujahid Muhammad tijjani Ambaliyar ruwa ta lalata yankuna 225 a kananan hukumomi 31 dake kano da jigawa a cewar hukumar bayar da again gaggawa ( NEMA) Babban jami'in NEMA mai kula da kano da jigawa, Dr.Nuradden Abdullahi ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Sanar. A cewarsa ambaliyar nada nasaba ne da ruwan Sama na mako da ake tafkawa tun daga watan yuli zuwa yanzu. Yace wannan yanayi Wanda ba yanzu aka soma fuskantar Saba, ya tilasrawa mutane da dana rasa matsuguni da sasu yin hijira zuwa wasu yankuna na Arewacin kasar. Kananan hukumomin da ambaliyar ruwan ta shafa a kano sun hada da Tudun Wada, Doguwa, Kibiya, Kiru, Gwale, Danbatta, Bagwai, Ajingi, Albasu, Shanono , Tsanyawa, Rimin Gado, da Dawakin Kudu. A jihar jigawa kuma akwai kananan hukumomi irinsu, Kafin Hausa, Malam Madori, Hadeja, Guri, Auyo, Birniwa, Jahun, Miga, Kiyawa, Birnin Kudu, Babura, ...